Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

19 Mayu 2022

18:52:43
1259036

​Najeriya: 'Yan Sanda Sun Kama Wadanda Suka Yi Garkuwa Da Daliban Jami'ar Greenfield

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargin suna da hannu wajen sace dalibai daga wata jami’a da ke arewacin kasar a shekarar da ta gabata, daya daga cikin sata da garkuwa da dalibai suka fi daukar hankali a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A ranar 20 ga Afrilun shekarar 2021, wasu ‘yan bindiga suka kashe wani ma’aikaci a yayin da suka kai farmaki jami’ar Greenfield da ke jihar Kaduna a arewa maso yammacin kasar, inda suka sace dalibai kusan 20.

‘Yan bindigar sun kashe biyar daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su cikin kwanaki kadan don tilastawa iyalai da gwamnati biyan kudin fansa, kafin daga bisani su saki ragowar dalibai goma sha hudu bayan kwanaki 40 a tsare.

Da yammacin ranar Larabar nan rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama wasu mutane biyu da suka hada Aminu Lawal, wanda aka fi sani da Kano, da kuma Murtala Dawu, wanda aka fi sani da Mugala – wadanda ke da hannu a wasu laifuka da dama na satar mutane.

Cikin sanarwar da ya fitar, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriyar Olumuyiwa Adejobi ya ce dukkanin mutanen biyu, sun amsa laifin yin garkuwa da daliban jami’ar Greenfield da ke jihar Kaduna, da kuma kashe biyar daga cikinsu kafin a biya su kudin fansa, su kuma su saki sauran.

Kakakin ‘yan sandan ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan bincike.

342/