Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

19 Mayu 2022

18:52:06
1259035

​Mutane 15 Aka Kashe A Wani Harin Ta’addanci Kan Iyakar Togo Da Burkina Faso

Kimanin mahara 15 ne aka kashe a makon da ya gabata, yayin wani hari a arewacin kasar Togo, a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Da sanyin safiyar ranar 11 ga watan Mayu ne kimanin mutane 60 dauke da makamai a kan babura sun kaddamar da wani “mummunan harin ta’addanci” a kan wani sansanin soji da ke Kebinkandi - kusa da kan iyaka da Burkina Faso, inda suka kashe sojoji takwas tare da raunata wasu 13, kamar yadda gwamnatin kasar ta sanar a lokacin.

“A cewar wata majiya mai tushe, an kashe mutane kusan 15 a cikin gungun maharan,” kamar yadda Ministan Tsaro na Togo Janar Damham Yark ya tabbatar da hakan.

Sojoji sun dakile wani harin da aka kai a watan Nuwamban bara a kauyen Sanluaga da ke arewacin kasar, lamarin da ya sa harin na makon jiya ya kasance na farko da ya haddasa asarar rayukaa cikin lokutan baya-bayan nan.

Tashe-tashen hankula daga kungiyoyi masu dauke da makamai da kungiyoyin masu da’awar jihadi na karuwa a yammacin Afirka.

342/