Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

19 Mayu 2022

18:49:37
1259031

Shugaban Kasar Nijer ya Ce Ficewar Mali Daga G5 Ya Kawo Karshen Kawancen

Shugaban Kasar Nijer Bazoum Muhammad ya bayyana cewa ficewar kasar Mali daga kawancen G5 Sahel ya kawo karshensa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - nakalto Muhammad yana fadar haka a lokacinda yake hira da wata jaridar kasar Faransa “La Croix” . ya kuma kara da cewa maida kasar Mali saniyar ware ya cutar da kawancen na G5 Sahel.

A wannan makon ne gwamnatin sojojin kasar Mali ta bada sanarwan cewa zata fice daga kungiyar ta G5 Sahel, saboda an hanata shugabancin karba-karba ba kawancen tare da umurnin wasu manya-manyan kasashen duniya.

A halin yanzu dai ‘yan ta’adda suna mamaye da wasu yankuna na kasashen Mali, Nijer da kuma Burkina Faso dake kan iyakar kasashen uku. Kafin haka gwamnatin kasar ta Mali ta bada sanarwan cewa ta murkushe wani yunkurin ya mata juyin mulki daga cikin kasar.

342/