Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Mataimakin fira ministan kasar Kuba Ricardo Ruiz ya jagorancin babbar tawaga zuwa kasar iran domin ganawa da manyan jami’an gwamnatin kasar da kuma halartar taron hadin guiwa kan tattalin arziki karo na 18. Domin kara bunkasa yanayin danagantakar tattalin arziki dake tsakanin kasashen biyu
Har ila yau shugaban na iran ya siffata dangantakar dake tsakanin Havana da Tehran a matsayin ta dabara, kuma ya bayyana irin bangarori daban –daban da iran za ta iya yin aiki tare da kasar ta cuba yadda za’aci gajiyar juna
Ana sa bangaren mataimakin fira ministan na Cuba ya mika sako ga shugaban iran na aniyar kasarsa na ganin an bunkasa dangantakar tattalin arziki da Cinikayya tsakaninta da kasar Iran.
342/