Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

18 Mayu 2022

19:34:03
1258765

Wakiliyar MDD, Ta Caccaki Takunkuman Amurka Kan Iran

Wakiliyar musamman ta Majalisar Dinkin Duniya, kan kare hakkin bil adama ta caccaki gwamnatin Amurka dangane da kakaba wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran takunkumi mai tsauri, tana mai cewa takunkuman tattalin arzikin na yin illa ga hakkin bil'adama a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Alena Douhan, wadda ke ziyarar aiki a Tehran, ta ce takunkuman na stawon shekaru sun shafi rayuwar al'ummar Iran gaba daya musamman bangaren masu karamin karfi na al'umma.

Jami'ar Majalisar Dinkin Duniya da ke aiki karkashin hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya, ta yi kira ga gwamnatin Washington da ta yi watsi da manufofinta na matsin lamba kan Iran da sauran kasashe.

A farkon wannan wata ne jami’ar ta MDD, ta fara ziyara a Tehran, inda ta gana da wakilan kungiyoyin farar hula da dama, da wakilan cibiyoyin hada-hadar kudi, jami'an diflomasiyya da dai saurensu.

Ziyarar kuma ita ce ta farko a Iran ta wani wakilin musamman na Majalisar Dinkin Duniya.

342/