Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

18 Mayu 2022

19:33:27
1258764

Sweden Da Finland Sun Gabatar Da Takardar Bukatarsu Ta Shiga NATO

Kasashen Finland da Sweden, sun gabatar da takardunsu ne neman shiga kungiysar tsaro ta NATO a wanann Laraba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kafin hakan dama Firaministar kasar Sweden Magdalena Andersson ta sanar cewa, kasashen, za su gabatar da takardarsu na neman zama mamban kungiyar.

Magdalena ta bayyana a yayin taron manema labarai da shugaban kasar Finland Sauli Niinisto dake ziyara a kasar cewa, mambobin kungiyar tsaro ta NATO za su karfafa tsaro a kasar Sweden da ma yankin tekun Baltic.

Ta kara da cewa, gabatar da aikace-aikacen hadin gwiwa tare da Finland, yana nufin za su iya ba da gudummawar tsaro a arewacin Turai.

Sai dai shugaban Rasha Vladimir Putin ya fada a ranar Litinin cewa, Moscow za ta mayar da martani, idan har NATO za ta tura kayayyakin aikin soji a yankunan Finland ko Sweden.

342/