Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

18 Mayu 2022

19:32:27
1258763

Rasha Ta Kori Gwamman Jami'an Diflomasiyyan Turai

Kasar Rasha ta sanar da korar jami’an diflomatsiyya faransa 34, a matsayin maida martani kan korar nata jami’an 41 da faransar ta yi a watan Afrilu da ya gabata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Rashar ta ba jami'an diflomasiyyar Faransa wa'adin mako biyu na su fice daga kasar.

Ma’aikatar harkokin wajen Rashar, ta gayyaci jakadan na faranasa a Moscow, inda ta mika masa takardar korar jami’an diflomatsiyan.

Baya ga Faransa, Rasha ta kuma kori jami’an diflomatsiyya Spain 27, da kuma na Italiya 24.

A nata bangare faransa ta yi tir da matakin tana mai cewa bai shi da wani tushe.

Tun bayan da kasar Rashar ta ce ta dauki matakin soji kan Ukraine, jami’anta diflomatsiyanta sama da 300 ne kasashen turai suka kora, saboda mamayar Ukraine.

342/