Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

18 Mayu 2022

19:31:42
1258762

Mali : An Cafke Mutum 7 Bisa Yunkurin Juyin Mulki

Hukumomnin rikon kwarya a Mali, sun ce suna tsare da mutum bakwai bisa zarginsu da hannu a yunkurin juyin mulki.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wasu majiyoyin shari’a sun ce an gabatar da mutanen a wata kotu dake shiya ta 6 a birnin Bamako a ranar Talata.

Ana zargin mutanen da yiwa tsaron kasar zagon kasa da kuma neman wargaza zaman lafiya a kasar.

Mafi akasarin mutanen sojoji ne wadanda mai mukami babba a cikinsu Kanal ne mai suna Amadou Keïta.

A ranar Litini ne gwamnatin riko ta kasar Malin ta sanar cewa, hukumar tsaron kasar ta cimma nasarar dakile wani yunkurin juyin mulki.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar, ta bayyana cewa, wasu sojojin kasar sun yi yunkurin juyin mulki ta matakan soja, a cikin daren ranar 11 zuwa 12 ga watan nan, kuma, wadannan sojoji sun sami goyon baya ne daga wata kasa ta yammacin duniya.

342/