Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

18 Mayu 2022

19:30:59
1258760

Turkiyya Na Kawo Cikas Ga Yunkurin Sweeden Da Filland Na Shiga Cikin NATO

Rahotanni sun tabbatar da cewa Turkiyya tana kawo cikas ga yunkurin Finland da Sweden na shiga NATO.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cewar kamfanin dillancin labaran DPA, kungiyar tsaro ta NATO ta kudiri aniyar a yau Laraba, ta tattauna bukatun da wakilan kasashen Finland da Sweden suka gabatar na shigar da kasashensu cikin kungiyar ta NATO, lamarin da ya zama yunkurinsu na farko domin shiga kungiyar ta NATO, amma saboda matsayin Ankara, tattaunawar ba ta cimma matsaya ba.

Bangaren Turkiyya ya jaddada cewa a halin yanzu ba za a amince da gudanar da taron ba.

Kasashen biyu dai sun kudiri aniyar shiga NATO ne biyo bayan fara ayyukan sojin kasar Rasha a cikin kasar Ukraine da ke makwabtaka da su, yayin da ita kuma Rasha ta sheda cewa shigarsu cikin NATO ba shi ne zai tabbatar musu da tsaro ba.

342/