Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

18 Mayu 2022

19:30:15
1258759

Raisi: Duniya Na Bukatar Sahihan Bayanai Kan Abubuwan Da Ke Wakana A Dukkanin Matakai

Da yake bayani a wajen taron koli na majalisar dake kula da yanar gizo a jiya da yamma yayi tsokaci kan yadda ake tunkarar ranar sadarwa da hulda da jama’a ta duniya, ya ce: a yanzu duniya tana bukatar bayanai kyauta kuma na gaskiya da kuma kare ra’ayin jama’a fiye da kowanne lokaci.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Yace kyakkyawar hulda da jama’a wani tsani ne na bunkasa wayewar Alumma da wayar da kan mutane kuma suna da muhimmiyar rawa da za’a su taka wajen wayar da kan alumma.

Har ila yau ya ce irin ci gaban da aka samu a fanni sadawarwa ba zai yi wahalar samar da kyakkawar mua’amala tsakanin Alumma ba, kuma zai tabbata ne ta hanyar yin amfani da dabarun zamani a bangaren hulda da jama’a, ci gaba da yin cudanya da jama’a musamman a gwamnatin dake ikirarin Adalci da farin jinni yana da matukar muhimmanci.

Adaidai lokacin da kasa take bukatar farfado da fata da mayar da hankali wajen daidaita tsarin zamantakewar alumma, wani nauyi ne da ya doru akan gwamanti na yin kyakkyawar hulda da jama’a.

342/