Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

18 Mayu 2022

19:25:56
1258754

​Iran: Babu Wani Ci Gaba A Tattaunawar Iran Da Saudia

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khadib Zadeh ya bayyana cewa babu wani ci gaba a tattaunawa ta baya-bayan nan tsakanin Iran da Saudia tare da shiga tsakani na kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - kasar Iran ya bayyana cewa ko wane bangare na da jerin bukatu a hannunta, amma babu wani abu da aka cimma tsakanin kasashen biyu.

Amma kakakin ma’aikatar harkokin wajen bai musanta cewa a kwai shirin haduwar ministocin harkokin wajen kasashen biyu nan gaba a birnin Bagadaza ba.

342/