Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

17 Mayu 2022

19:36:24
1258440

​Khatibzadeh: Babu Wani Abu Da Zai Iya Wargaza Alakar Iran Da Rasha

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Khatibazab, yayin da yake magana kan huldar da ke tsakanin Iran da Rasha ya ce, ba za mu taba bari wani abu ya wargaza wannan alakar ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A wata hira da kamfanin dillancin labaran kasar Rasha RIA Novosti kakakin ma'aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Saeed Khatibzadeh ya bayyana cewa, fadada kungiyar tsaro ta NATO da kuma rashin mutunta batun tsaron kasar Rasha shi ne dalilan abin da yake faruwa a kasar Ukraine.

"Muna tunanin cewa tushen duk wani abu da muke gani a yau, wato fadada kungiyar tsaro ta NATO ko kuma rashin mutunta yarjeniyoyi na kasa da kasa da kasashen Turai ke yi, da kuma watsi da batun siyasa da tsaro na sauran kasashe musamman wadanda suke takun saka da su, shi ne tushen dukkanin fitintinua duniya" in ji Khatibzadeh.

Har yanzu Iran tana ci gaba da kokarin samar da fahimtar juna tsakanin Rasha da Ukraine, kasantuwar dukkanin kasashen biyu suna da kyakkayawar alaka da kasar ta Iran.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewar Iran na shirin kaddamar da wasu sabbin shawarwari kan hakan, da ke nufin sasanta tsakanin tsakanin Rasha da Ukraine.

Ya ce alaka tsakanin Rasha da Iran tana nan daram, kuma babu wani abu da zai iya ruguza wannan alaka.

342/