Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

17 Mayu 2022

19:33:39
1258437

​Lavrov: Ukraine Tana Zartar Da Manufofin Kasashen Turai Ne Amma Ba Ta Da ‘Yancin Siyasa

Ministan harkokin wajen Rasha ya ce Ukraine ba kasa ce mai cin gashin kanta ba, ko da kuwa Kyiv ta yi ikirari da hakan, kuma kasashen yammacin duniya ba sa bukatar ta zama mai cin gashin kanta, domin tana aiwatar da manufofinsu ne musamman domin cutar da Rasha.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata, ministan harkokin wajen Rasha ya tabbatar da cewa Moscow na da labarin cewa bangaren Ukraine a tattaunawar yana karkashin ikon London da Washington, saboda haka gwamnatin Ukraine ba za ta iya yanke shawara kan wani abu day a sabawa Amurka ko Burtaniya.

"Muna da bayanin da ke isar mana ta tashoshi daban-daban cewa Washington da London ne ke jagorantar masu yin shawarwarin Ukraine ." in ji shi.

Lavrov ya yi nuni da cewa, kasashen Yamma ba sa bukatar kasar Ukraine, sai dai saboda kasa ce mai amfani gare su ta fuskar yin amfani da ita domin cimma manufofi na siyasa da kuma tsokana.

Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa kasashen yammacin duniya ba a shirye suke ba su bayar da tabbacin tsaro ga Ukraine, amma dai za su yi amfani da ita da kuma kafofin yada labaransu domin cimma wannan buri nasu.

342/