Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta bayyana cewa mafi yawan kasashen sun dora laifin rashin fahintar junan kan kasar Hungaria, wacce ta ki amincewa a kara fadada takunkuman sayan makamashi daga kasar Rasha.
Labarin ya kara da cewa a taronsu na jiya Litinin kasashen na EU sun amince da karin tallafi na makamai ga kasar Ukrain na Euro miliyon 500 wanda ya zuwa yanzu kungiyar ta bada makamai na kimanin Euro billiyon 2 kenan.
Masana tattalin arziki sun bayyana cewa kungiyar EU tana fuskantar karancin makamashi sanadiyyar takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa Rasha, a dai dai lokacinda rayuwa take kara tsada ga mutanen nahiyar ko da kuwa na wani lokaci ne.
342/