Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kamar da yadda kungiyar ta Nato ta bayyana, Atisayan zai ci gaba har zuwa nan da ranar 3 ga watan yuni mai kamawa, kuma ta ce babban makasdudin gudanar da atisayin na hadin guiwa shi ne don kara nuna irin shiri da hadin kai da kasashen da ke mambobi a kungiyar suke da shi ,
kimanin dakarun soji 15000 ne suke gudanar da Atisayin a Estoniya daya daga cikin mafi girma da aka taba yi tun a shekara ta 1991. Kuma ana gudanar da shi ne a wani wuri ai nisan kilomita 64 da sansanin sojin kasar Rasha.
shugaban kasar Rasha Vialdmir Putin yace Kasancewar Finland da Sweden a cikin kungiyar tsaro ta NATO baya wata barazana ga kasar Rasha, sai dai zai mayar da martanin da ya dace kan matakin da wadannan kasashen suka dauka.
342/