Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Da yake wa Alummar kasar bayani shugaban yayi tsokaci kan banbance-banbancen da aka kasa warwarewa tsakanin gwamnati da bangaren majalisar, wannan ya say a bukaci a gudanar da zaben yan majalisu a watan Decemba mai kamawa,
Ya ce na yanke shawarar kara bada dama ga Alummar kasar Guinea domin su sake bayyana a gaban akwatunan zaben a cikin wannan shekara domin zaben yan majalisun da suke so su wakilcesu a karo na 11
Jam’iyar PAIGC ce ta mamaye kujerun majalisar dokokin kasar , inda jami’iyar da shugaban kasar Embola ke jagoranta ta Modem G-15 ba ta samu mafiyawancin kujeru a majalisar ba a zaben da aka yi a sehakra ta 2019 ba da hakan ya kara zafafa zaman tankiya tsankin majalisa da bangaren zartarwa a kasar.
342/