Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Haka zalika tattaunawa kan wasu batutuwa na daban da suka shafi dangantakar dake tsakanin kasashen, da kuma yadda za’a warware wasu matsalolin da iraniyawa mazauna kasar suke fuskanta suna daga cikin abubuwa da suka mamye tattaunawar ta su.
Da yake bayani game da ganawar ta su da sabon shugaban hadaddiyar Daular larabawa ministan harkokin wajen iran kyakkyawar alakar dake tsakanin kasahen biyu makwabtan juna a matsayin babban abin da yake batawa makiya rai a yankin
Daga karshe ya ce an bude sabon shafin dangantaka tsakanin kasashen biyu kuma muna mika hannun abota da kauna ga makwabtanmu, kum kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yana kunyata makiyan yankin.
342/