Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Talata

17 Mayu 2022

19:20:44
1258426

Putin: Fadadar NATO, Zuwa Sweden Da Finland, Zai Fuskanci Martani

Shugaba Vladimir Putin, na Rasha, ya bayyana cewa, wanzuwar kungiyar tsaro ta NATO, zuwa kasashen Sweden da kuma Finland, zai fuskanci martani daga kasarsa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Mista Putin, ya bayyana hakan ne yau Litinin yayin wani taro na tsakanin Rasha da kawayenta na yankin da take kawance dasu a fannin soji.

Furucin na Putin, na zuwa ne bayan da kasashen na Sweden Da Finland, suka bayyana shirinsu na kasancewa mamba a kungiyar ta Nato.

Saida Putin, ya ce shigar wadanan kasashen a NATO, ba barazana ne ba ga kasarsa nan take, amma Rashar za ta maida martani ga bazuwar kayayakin soji a cikin wadanan kasashen, wanda kuma zai fuskanci martani.

342/