Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

16 Mayu 2022

15:42:24
1258154

Iran : Kasashe Masu Karfi Na Amfani Da Hakkin Dan Adam Wajen Cimma Muradun Siyasa

Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Saed Khatib Zade da yake ganawa da wasu kungiyoyi masu zaman kansu a cibiyar kula da tattalin arziki da zamantakewa na majalalisar dinkin duniya ya fadi cewa kare hakkin bil adama yana daya daga cikin abin da ake fakewa dashi wajen cimma manufofin siyasa a dangantakar kasa da kasa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Har il yau ya kara da cewa gwamnatin Amurka ta bata sunan hakkin dan Adam inda take amfani da shi amatsayin wani makami na cimma manufofinta da hakan ya rusa kimar kare hakki bil adama

Kakakin ya bayyana cewa ma’aikatarsa a shirye take ta taimakawa kungiyoyin domin kare mutunci da matsayinsu ahukumar ECOSOC da ma matakin kasa da kasa.

Sama da kunguyoyin masu zaman kansu guda 80 ne suka halarci wajen taron, inda mataimakin minsitan shari’an na kasar iran kan harkokin kasa da kasa Kazem Gharibabadi ya yi jawabi a wajen taron.

342/