Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

16 Mayu 2022

15:40:50
1258152

Kasar Mali Ta Sanar Da Ficewa Daga Dakarun Hadin Guiwa Na Yankin Sahel

Gwmantin sojin kasar mali ta fitar da sanarwar ne a jiya haladi ina ta ke cewa za ta fice daga cikin gamayyar dakarun yaki da kungiyoyi masu ikirarin jihadi a yankin Sahel wato G5 bayan da aka hana kasar karbar jagorancin kungiyar a yankin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - kungiyar ta G5 ne bayan da aka mayar da ita saniyar ware da kuma takunkumi da kasashe dake makwabtaka da ita suka kakaba mata tuna watan janerun da ya gabata saboda da jan kafa da take yin a mayar da kasar kan turbar Demukuradiya,

Dangantakar mali da sauran kasahen yamma musamman babbar kawarta da ta taba yi mata mulkin mallaka wato kasar farasan ta kara tabrbarewa ne bayan da gwamnatin sojin ta karfafa dangantakarta da kasar Rasha.

A farkon wannan watan ne babban maga takardan majalisar dinkn duniya Antonio Gutteres ya bayyana cewa matsalolin siyasa da take hakkin bil adama a kasashen mali da borkina faso suna yin kafar Ungulu a kokarin da ake yi na yaki da masu ikirarin jihadi a yankin sahel, kuma yayi da kira da a koma mulkin farar hula cikin gaggawa.

342/