Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

16 Mayu 2022

15:38:51
1258150

​Iran: Hukumar Hajji Da Ziyara Ta Bada Sanarwan Cika Adadin Da Saudiya Ta Warewa Kasar A Hajjin Bana

Shugaban hukumar hajji da ziyara Sayyid Safi Husaini ya bayyana cewa hukumarsa ta kammala dukkan shirye-shirye na gudanar da ayyukan hajji da umra na wannan shekra.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kafin haka mataimakin shugaban hukumar Akbar Rizayi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Saudiya ta warewa mahajjatan Iran mutane 39,635 kacal.

Labarin ya kara da cewa twaga ta farko zata fara barin Iran zuwa Madina ne a 13 ga watan Yulin wannan shekara sannan a kammala aikin su fara dawowa a ranar 29-Yuli na wannana shekara.

Banda haka labarin ya kara cewa tuni hukumar ta fara aikin neman masauki da wuraren cin abinci da magunguna na ma’aikata a hajjan wannan shekara.

342/