Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

16 Mayu 2022

15:31:44
1258145

​Kasar Sweden Ta Bayyana Bukatarta Ta Shiga Kungiyar Tsaro Ta NATO

Kasar Sweden Ta Bayyana anniyarta na shiga kungiyar tsaro ta NATO bayan da mafi yawan yan majalisar dokokin kasar suka amince da hakan. Da wannan kuma kasar ka kawo karshen adawa da shiga kungiyar wacce jam’iyyar social Democratic mai mulkin kasar ta yi ta nunawa a baya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Banda kasar Holanda kasar Finland ma tana kan hanyar gabatar da bukatarta na shiga kungiyar tsaron.

Labarin ya kammala da cewa a jiya Lahadi 15 ga watan Mayu ne majalisar ta gudanar da taron amince da bukatar shiga kungiyar tan NATO.

Kasashen Turai na gabas fiye da 10 ne suka shiga kungiyar Tsaro ta NATO tun bayan rushewar tarayyar Sovied a shekara ta 1991. Kafin rushewar tarayyar dai gwamnatin kasar Rasha ta kasashen yamma kada su fafa kungiyar Nato daga kasashen gabacin Turai.

Day daga cikin dalilanyakin Rasha a ukrain sun hada da jinine batun shiga kungiyar tsaro ta Nato.

342/