Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

15 Mayu 2022

16:30:47
1257822

​Najeriya: ‘Yan Ta’adda Sun Saki Fasinjan Jirgin Kaduna Mai Ciki Saboda Tausayi

Wata mata mai ciki daga cikin fasinjojin jirgin kasa wanda ‘yan ta’adda suka farwa a ranar 28 ga watan Maris shekara ta 2022 da ta sami ‘yancin kanta bayan da yan ta’adda suka sallameta saboda jin kai.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar Leadership ta Najeriya bata fadi sunan matar ba, amma ‘yan ta’addan sun tilasta mata fita a wasu hotunan Bidiyo inda take godewa yan ta’addan sannan ta yi kira ga gwamnatin kasar ta tattauna da ‘yan ta’addan don samun sakin sauran fasinjojin da suke rage a hannunsu.

Wannan dai shi ne mutum na uku wanda ya ta’addan suka sallama. Da farko akwai Alwan Hassan manajar bankin noma BOA da Sadik ABdullahi Ango dan shugaban majalisar dattawan Arewa, bayan sun biya kudaden fansa wadanda suka fi naira miliyon 100.

342/