Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

15 Mayu 2022

16:29:04
1257820

​A Yau Lahadi Ne Ake Zaben Shugaban Kasa A Kasar Somaliya

A yau lahadi ne ake saran majalisar dokokin kasar Somaliya zata zabi shugaban kasa a cikin ‘yan takara 39 da suke neman wannan kujerar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayyana cewa fitattun ‘yan takara a zaben shugaban kasa na yau a kasar Somalia su ne shugaba mai ci Mohammad Abdullahi Farmajo, da kuma wasu tsoffin shuwagabbanin kasar guda biyu, Hasan Sheikh Mahmood da kuma Shareef Sheikh Ahmad.

Banda haka hatta firai ministan kasar mai ci Hassan Ali Khairi na daga cikin ‘yan takarar neman kujerar shugabancin kasar.

Majalisar dokokin kasar Somalia ce zata zabi shugaban kasa saboda irin matsalolin tsaron da suke addabar kasar idan an ce mutane ne zasu zabe shi kai tsaye. Dan takaran mai nasara a zaben nay au shi ne wanda mafi rinjayen yan majalisa kasar 329 suka zaba.

Labarin ya kara da cewa yakamata a ce an gudanar da zaben tun da dadewa, amma matsalolin yadda za’a gudanar da zaben da sabani tsakanin ‘yan siyasar kasar ya jinkirta zaben har zuwa yau 15 ga watan Mayun shekara ta 2022.

342/