Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

15 Mayu 2022

16:23:22
1257814

Najeriya : An Kafa Dokar Hana Fita A Sokoto Bayan Barkewar Zanga zanga

Gwamnatin Jihar Sokoto ta saka dokar hana fita ta tsawon awa 24 a jihar sakamakon zanga-zangar da wasu mazauna jihar suka gudanar a yau Asabar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta ce dokar za ta fara aiki nan take.

An dauki matakin ne "saboda dawo da doka da oda a birnin Sokoto da jihar baki daya", a cewar sanarwar.

Masu zanga-zangar na neman jami'an tsaro dasu saki mutanen da suka kama da ake zargi da kisan matashiya Deborah Samuel wadda suka zarga da batanci wa Annabi Muhammadu (SAW).

A jihar Kaduna ma Gwamnan Jihar Nasir El-Rufai ya haramta gudanar da "zanga-zangar addini" game da batun.

Sanarwar da ma'aikatar harkokin cikin gida ta Kaduna ta fitar ta ce an dauki matakin "saboda yukurin wasu marasa kishin kasa" na shirya zanga-zangar adawa da kuma goyon bayan lamarin.

342/