Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

14 Mayu 2022

19:21:58
1257514

​Najeriya: Shugaba Buhari Yayi Allawadai Da Kissan Wata Daliba Kirista A Sokoto .

Shugaban Muhammadu Buhari ya yi allawadai da kissan da wasu jama’a suka yiwa wata daliba, wanda take shekara ta biyu a kolajin Shehu Shagari ta tarbiyyan malamai dake sokoto a ranar Alhamis.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto shugaban yana fadar haka ta bakin mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin watsa labarai Malaman Garba Shehu.

Shugaban ya ce bai kamata mutane su dauki doka a hannunsa ba ko da kuwa hakan ya faru. Haka ma mataimakin shugaban kasa Proff. Yeme Osingbajo ya nuna takaicinsa dangne da kissan Deborah Samuel kan zargin batanci da manzon All..(s). Osingbaji ya kara da cewa, akwai abin takaita da yadda mutane suke daukar doka a hannunsu, bayan ga akwai hukumomin da yakata su kula da irin wannan lamarin.

Daga karshe ya bukaci a gaggauta zakulo wadanda suka yi hakan sannan a hukunta su. Sannan ya mikla ta’ziyya ga iyalan Deborah Samuel wacce aka kashe a sokoto.

342/