Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

10 Mayu 2022

15:02:38
1256418

Rasha Ta Ja Kunnen Kasashen Yamma Dangane Da Amfani Da Kadarorinta Don Sake Gina Ukrain

Kamfanin dillancin labaran Sput News na kasar Rasha ya nakalto mataimakin ministan harkokin wajen kasar yana cewa mayarwa kasar Ukrain kadarorin Rasha da kasashen suka kwace baya bisa ka’ida kuma zai kawo illa babban a tsarin bankuna na zamani, sannan kasashen turai ne zasu fi cutuwa idan sun yi haka.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kafin haka dai jami’ii mai kula da al-amuran harkokin waje na kungiyar tarayyar Turai Joseph Barrel ya bayyana cewa kasashen turai suna iya amfani da kadarorin kasar Rasha ta suka kwace wajen sake gina kasar Ukrai idan a gama yakin.

A ranar 24 ga watan Fabrairu da ya gabata ne kasar Rasha ta fara abinda ta kira aikin soje na musamman a kasar Ukrain, da nufin kwance damarar yakin kasar da tabbatar da ‘yencin yankun Dombos da ya balle daga kasar ta Ukrain. Ya zuwa yanzu dai kasashen Yamma sun dorawa kasar Rasha takunkuman tattalin arziki har sau biyar don karya karfinta na yaki a ukrain.

342/