Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

10 Mayu 2022

14:59:56
1256416

​Rasha Na Gudanar Da Bukuwan Tunawa Da Nasarar Tarayyar Soviet A Kan ‘Yan Nazy

A yau ne ake gudanar da bukukuwan tunawa da samun nasarar da dakarun tarayayr Soviet suka samu a kan ‘yan Nazy a lokacin yakin duniya, wanda shi ne karo na 77 da ake gudanar da wannan taro na shekara-sheakara.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ne ya jagoranci bude bukukuwan a yau a birnin Mascow, inda ya gabatar da jawabi kan ranar da kuam muhimmancinta ga al’ummar kasar Rasha.

Putin ya ce ba za su manta da sadaukarwar da sojojin tarayyar Soviet suka yi ba wajen kawo karshen barazar ‘yan Nazy, haka nan kuma Putin ya yi ishara da sake bayyanar wadanda ya kira sabbin Nazy a Ukraine a kan iyakokin kasar Rasha.

Ya ce matakin da Rasha ta dauka na gudanar da ayyukan soji domin kawo karshen barazanar tsaro da take fuskanta daga kasashen NATO a kan iyakokinta shi ne abin da yafi dacewa, kuma hakan daidai ne.

Tun a shekara ta 1943 sojojin Nazi suka fara ganin koma-baya a yakin duniya na biyu, daga karshe sojojin tarayyar Soviet daga gabas sun shiga birnin Berlin babban birnin kasar Jamus a farkon shekara ta 1945.

Sai dai kasashen kawance sun ci gaba da yakar Japan wadda take mara baya ga Jamus a yakin har zuwa watan Augustan 1945, inda Amurka ta jefa makaman nukliya kan kasar ta Japan, wanda hakan yasa ta mika wuya.

An dauki shekaru 6 ana yakin duniya na biyu, an kashe mutane miliyin 60, sannan an yi asarar dukiyoyi na kimanin dalar Amurka trillion 1.15

342/