Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

8 Mayu 2022

15:08:59
1255811

Allah Ya Yi Wa Kakakin Majalisar Dokokin Ivory Coast Rasuwa

A Ivory Coast, an shiga alhini game da rasuwar kakakin majalisar dokokin kasar Amadou Soumahoro.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Fitaccen dan siyasa a kasar, kuma daya daga cikin amintattun shugaban kasar Alhasan Ouatara, Amadou Soumahoro, ya rasu jiya Asabar yana da shekara 68 a duniya, kamar yadda fadar shugaban kasar ta sanar.

Ya jima da yake fama da rashin lafiya, wanda ya sanya yake fita ketare neman magani, saidai a hukumance ba’a taba bayyana abunda ke damunsa ba.

Rashin lafiyar dake damunsa shi ya sanya ya mika shugabancin majalisar dokokin kasar ga mukadashinsa.

Mirigayin yana kuma daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar RDR, mai mulki wacce ta koma RHDP a yau, Yana kuma shugabancin majalisar ne tun cikin shekarar 2019, har zuwa jiya da Allah ya yi masa rasuwa.

342/