Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

7 Mayu 2022

19:06:26
1255502

A Karon Farko Kwamitin Tsaron MDD Ya Cimma Matsaya Kan Warware Rikicin Ukraine Ta Hanyar Lumana

A karon farko dukkanin mambobin Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya sun amince kan warware matsalar Ukraine ta hanyar lumana.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya baki dayan mambobinsa sun amince da wata sanarwa a ranar jiya Juma'a mai nuna goyon baya ga kokarin babban magatakardar majalisar, na neman hanyar warware matsalar Ukraine cikin lumana, wanda shi ne karon farko da aka samu amincewar dukaknin kan wannan batu, wanda Mexico da ke jagorantar shugabancin kwamitin c eta gabatar da shawarar.

Kamfanin dillancin labaran AP ya ce, ya samu takardar sanarwar wadda ke cewa; "Kwamitin sulhun ya bayyana goyon bayansa ga kokarin da babban sakataren yake yi wajen neman mafita a kan batun Ukraine ta hanyar lumana.”

Haka nan kuma rahoton na AP ya ce sanarwar ba ta ƙunshi kalmomi irin su "yaki," "rikici," "mamaye" ko "aikin soji na musamman," ba.

Amurka ta kuma bukaci Sakatare-Janar Antonio Guterres da ya gabatar da jawabi ga Kwamitin Sulhu kan wannan batu.

Wakilin dindindin na Mexico na Majalisar Dinkin Duniya Juan Ramón de la Fuente Ramírez ya shaida wa kamfanin dilalncin labaran TASS cewa, Rasha a shirye take a warware wannan batu ta hanyar diflomasiyya.

342/