Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

6 Mayu 2022

19:02:15
1255150

Sarkin Sokoto: Ba Za Mu Bari Yan Ta’adda Su Ci Gaba da Yin Abin Da Suka Ga Dama Ba

Sarkin Musulmin Saadu abubukar na 3 ya bayyana hakan ne, lokacin da yake jawabi, jim kadan bayan kammala jawabin da shugaban rundunar sojoji Nijeriya Laftanar-Janar Faruk Yahaya, ya yi lokacin da ya kai masa ziyarar gaisuwar sallah.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ya ce, idan aka ci gaba da sassauta musu, don ana kiransu ‘yan ta’adda, ba zai haifar wa da al’ummar kasar nan da mai ido ba. Saboda haka, dole ne a dauki tsauraran matakai a kansu domin ganin bayansu

Harila ya ya kara da cewa” Dole ne mun canja salon yaki tare da daukar sabbin matakai wajen kawo karshen wannan ta’addanci da ‘yan ta’adda a dukkan fadin kasar nan. Kamar yadda shugaban kasa ya fada a ranar sallah, cewa, ayyukan ‘yan ta’addar ya kai makura.

Tun da farko dai, faruk, ya yi alkawarin haduwa da kasurgumin dan ta’addar na Bello Turji da sauran wasu ‘yan ta’addar da ke addabar Arewa maso yamma kan su ajiye makamansu.

Da ya ke tsokaci kan sauran ‘yanta’addan musamman wadanda ke yankin karamar hukumar Isa, ta jihar Sakkwato ya ce, yanzu haka dukkan ‘yan ta’addar da ke wannan yanki na cikin tashin hankali, domin kuwa karshensu ya zo, yanzu haka an shiga dukkan maboyarsu an tarwatsa su.

342/