Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

6 Mayu 2022

18:53:19
1255147

“Yan Jarida Sun Yi zanga-Zangar Neman “Yanci Yan Jaridu A Kasar Tunusiya

Ajiya Alhamis ce yan Jaridu a a kasar Tunusiya suka yi zanga-zangar nuna adawa da abin da suka kira nuna danniya da Tursasawa yan Jaridu da hana furta albarkacin bakinsu tun bayan da shugaban kasar Kais Said Ya karbi mulki a kasar a bara.

ABNA24 : kungiyar yan jaridu ta kasa SNJT ta fadi ce wa ta shirya Zanga-zangar ce domin yi tayi tir da matakin da tace mahukumta take yi na takurawa kafafen watsa labarawa da mayar da su hanyoyin farfaganda, masu zanga zangar sun rika rera taken neman yanci da nuna rashin amincewa da danniya

A watan yulin day a gabata ne Saed ya rusa gwamnatin da kuma dakatar da majalisar dokokin kasar , wanda tun daga lokacin yake amfani da dokoki na kama karya irin na soja, kuma ya karbe ikon kula da hukumomi da bangaren shri’a na kasar da hukumar zabe ta kasar.

Ana ta bangaren mataimakiyar shugaban kungiyar yan jaridu ta kasar Amira Mohammad ta gargadi game da babban hadarin da ke tunakarar aikin jarida a kasar , hakika yanci yan jaridu yana cikin hadari a kasar.

Tace daga lokacin da Saied ya karbe madafun iko zuwa yau bai taba yin taron manema labarai ba ko da sau daya da hakan ke nuna irin manufofin siyasar da bata damu da kula hakkin yan kasa ba wannan shi ne abin da ke faruwa a kasar Tunusiya acewarta.

342/