Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

5 Mayu 2022

21:35:18
1254904

​Najeriya: Kamfanonin Sadarwa Na Shirin Kara Kudin Hidimomi Ga Masu Amfani Da Wayoyin Salula

Kamfanin sadarwa masu zaman kansu a tarayyar Najeriya suna shirin kara farashin khidimomin da suke wa wadanda suke amfani da wayoyin sadarwa da hannu a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar Leadership ta Najeriya ta bayyana cewa kamfanonin sun rubutawa hukumar sadawa ta kasa NCC wasika inda suke bukatar amincewarta don kara kimani kasha 40 na farashin khidimomin da suke wa masu amfani da woyoyin sadarwa a kasar saboda yawan kudaden da suke kashewa don tafiyar da kamfanoninsu a kasar.

Labarin ya kara da cewa kamfanonin suna bukatar kasar kudin buga waya ya tashi daga N6.4 zuwa N8.95, sai kuma aika sako a rubuce wato (SMS) daga N4 zuwa N5.61, har’ila yau kamfanonin suna son kara farashin internet da suke bawa masu amfani da wayoyin sallula a kasar.

Tuni dai mutane suka fara nuna korafinsu dangane da wannan kokarin da kamfanonin suke yi, ganin irin tsadar rayuwa da suke fama da shi a kasar.

342/