Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

5 Mayu 2022

21:33:47
1254900

Sakataren MDD Ya Kammala Ziyara A Najeriya Kuma Ya Bukaci A Taimakamata

Ajiya laraba ce sakataren janar din Majalisar dinkin Duniya Antonio Guttress ya kammala ziyara aiki da ya kai Najeriya , inda ya rufe ziyarar tasa a fadar shugaban kasar, tare da ganawa da shugaban na Najeriya mohammadu Buhari ,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Gutteres ya bukaci a taimakawa Najeriya da Karin kudi da yawansu ya kai dala miliyan 351 da zai zama jimmillar kudi dala biliyan 1.1 domin gudanar da Ayyukan Agaji da kasar ke yi, yace duk da irin abubuwan da na gani amma mutane suna da burin ganin sun koma gidajensu domin ci gaba da rayuwa.

Ana sa bangaren shugaban Najeriya ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da yaki da Ta’addanci kuma yayi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su taimaka wajen ganin an kawo karshen tsatsauran ra’ayi.

Idan ana iya tunawa tun a ranar Litinin Guttres ya ziyarci cibiyoyin yan gudun hijira na wadanda rikicin boko Haram ya raba da mahalli dake cikin garin Maiduguri na jihar Borno.

342/