Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

4 Mayu 2022

19:05:34
1254559

(EU), Na Shirin Haramta Sayen Man Fetur Din Rasha

Kungiyar tarayyar turai ta sanar da shirin kasashe mambobinta na sake kakaba wa Rasha takunkumi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Da take bayyana hakan shugabar hukumar tarayyar Turan, Ursula von der Leyen ta ce matakin ya tanadi har da haramta sayen man fetur din kasar ta Rasha a 'yan kwanaki masu zuwa.

Mrs Ursula von der Leyen ta ce kungiyar za ta dakatar da dogaron da take yi da fetur din Rasha.

Sai dai EUn ba ta kai ga cimma matsaya ba kan batun daina sayen iskar gas daga Rasha, saboda yadda wasu kasashen turan suka dogara da shi.

Batun kakaba wa Rasha takunkumi kan makamashinta ya haifar da rarrabuwar kai tsakanin kasashen na yamma.

342/