Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

4 Mayu 2022

19:04:06
1254557

Somaliya Ta Yi Tir Da Harin Al’Shabab Kan Dakarun AU

Gwamnatin Somaliya ta yi Allah wadai da harin da aka kai sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar AU a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A jiya ne, kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta al-Shabaab a Somaliya, ta kai hari kan wani sansanin sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka da ke jihar Shabelle na tsakiyar Somaliya.

A cewar kafar yada labaran kasar, kungiyar ta kashe wani adadi mai yawa na dakarun dake sansanin.

An yi imanin cewa, kungiyar al-Shabaab na da alaka da kungiyar al-Qaeda, kuma tana neman hambarar da gwamnatin Somaliya.

A shekarar 2011, dakarun kungiyar tarayyar Afirka, sun yi nasarar fatattakar mayakan na al-Shabaab daga Mogadishu, amma har yanzu kungiyar masu tsattsauran ra'ayin, na rike da yankuna da dama na yankunan karkarar Somaliya inda suke yawaita kai hare-hare a kusa da Mogadishu da makwabciyarta kasar Kenya.

342/