Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

4 Mayu 2022

19:02:57
1254556

‘Yan Takara 46 Zasu Fafata A Zaben Shugaban Kenya

A Kenya, ‘yan takara 46 ne zasu fafata a zaben shugabancin kasar na watan Agusta mai zuwa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Manyan Jam’iyyu a zaben sun hada da (ODM), ta tsohon firaministan kasar Raila Odinga, dake samun goyan bayan shugaban kssar mai barin gado, Uhuru Kenyatta, da kuma Jam’iyyar (UDA), ta fira minsitan kasar mai ci William Ruto.

A ranar 9 ga watan Agusta mai zuwa ne za’a gudanar da zaben shugaban kasa gami da mataimakin shugaban kasa a kasar ta Kenya.
Kasar ta saba fuskantar rikice rikicen bayan zabe masu nasaba da kalubalantar sakamakon manyan zabuka.

342/