Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Parstoday
Laraba

4 Mayu 2022

18:48:53
1254542

​Ukrain: Sojojin Rasha sun Wargaza Cibiyoyin Soje Har 37 A Jiya Litinin A Ukrain

Kakakin ma’aikatar tsaro na kasar Rasha ya bayyana cewa a jiya Talata jiragen yakin kasar sun kai farmaki kan cibiyoyin sojoji guda 37 a cikin kasar Ukrain kuma sun lalatasu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - nakalto Oghoor Konshankuf yana fadar haka a jawabinsa da ya saba gabatawa a ko wace rana a jiya Talata.

Labarin ya kara da cewa sojojin Ukrain kimani 210 suka rasa rayukansu.

A dai dai lokacin da aka shika kwanaki na 17 kenan da fara yaki a kasar Ukraim, rahotanni sun bayyana cewa mutanen akalla miliyon 3,700,000 ne aka tabbatar da cewa sun fice daga kasar, sannan wasu 1,070 kuma suka rasa rayukansu.

Rasha ta shiga yaki a Ukrai ne da nufin kwance damarar yakin ta, hanata shiga kungiyar nato, sannan da bellewar yankunan Dombas daga kasar.

342/