Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

2 Mayu 2022

12:54:51
1254172

Sudan: Shugaban Kasa Ya Bukaci ‘Yan Adawa Su Ajiye Bambance-Bambance Tsakaninsu Da Gwamnati

Shugaban majalisar mulki ta kasar Sudan Abdulfattah Alburhan ya yi kira ga gamayyar jam’iyyun adawar kasar zuwa hadin kai da kuma ajiye dukkan bambamce-bambance da ke tsakaninsu don kafa gwamnati.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Aljazeera dake kasar Qatar ta nakalto Janar Burhan yana fadar haka a sakonsa na taya mutanen kasar murnar sallar Idi karama.

Har’ila yau labarin ya kara da cewa shugaban ya bayyana cewa a shirye yake ya hada kai da dukkan jam’iyyun siyasa wadanda suke son ci gaban kasar Sudan da kuma ganin cewa ta fita daga cikin matsalplom da ta fama da su a halin yanzu.

A wani bangare kuma shugaban Burhan y ace dole ne a sauya wasu dokokin kasar saboda kawo karshen rikicin kabilanci wanda ya ki ci yaki cinyewa a wasu sassan kasar.

342/