Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

2 Mayu 2022

12:53:58
1254171

An kama Wasu Mutane 3 Masu Kai Wa ‘Yan Boko Haram Bindigogi A Tafkin Chadi

Gamayyar sojojin Nijeriya da na kasashen waje (MNJTF), sun samu nasarar cafke wasu mutum uku da suke safarar makamai zuwa Nijeriya ta iyakokin Kamaru da Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan ne Yasa sojojin suka kai farmaki inda suka samu nasarar cafke wadanda ake zargin da wannan aika I aika, ya ce makaman da aka kama sun hada da bindiga kirar AK-47 wanda ake shirin ake wa zuwa sansanin ‘yan Boko Haram.

Tuni Sojojin suk yi awun gaba da wadanda suka kama domin kara zurfafa bincike a kansu. Sojojin sun bayyana irin nasarorin da suke samu akokarin da ake na dakile hare-haren ‘yan Boko Haram.

342/