Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Rikici ya barke ne tsakanin wasu matasa da suke sanya da bakaken kaya da jami’an yan sanda inda aka farfasa tagogin shaguna inda wuta take ta fitowa, inda suke dauke da kwaleye da aka zana kalaman nuna adawa da tsarin jari hujja, wannan yasa yan sanda suka yi amfani da barkunon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar
Su mana masu adawa da manufofin siyasar Makron sun yi zanga-zangar nuna adawa das hi a kan tituna a birane daban –daban na kasar faransa a lokacin yakin neman zabe da kuma ranar da aka gudanar da zabe a aksar, inda a zagaye na biyu ne Makron ya kayar da abokiyar hammayarsa Marine Le pen da hakan ya bashi damar ci gaba da kasancewa a kujarar shugabancin kasar.
342/