Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

2 Mayu 2022

12:49:51
1254167

Za’a Kafa Sabon Kwamiti Da Zai Rubuta Sabon Kundin Tsarin Mulki A Kasar Tunusiya

A wani jawabi ta gidan talabijin da Shugaban kasar Tunusiya Kais Said ya yi wa Alummar kasar a jiya Lahadi ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta kafa wani kwamiti da zai rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar na sabuwar gwamnati a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ya ce nan day an kwanaki masu zuwa za’a rubuta sabon kundin tsarin mulkin sannan kuma za’a taron tattaunawa na kasa wanda zai kunshi manyan kungiyoyin kasar da kungiyoyin kwadago dana lauwoyi , dama kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar, kuma za’a kada kuri’ar jin ra’ayin jama’a kan sabon kundin tsarin mulkin a ranar 25 ga watan yuli mai kamawa.

Shugaban kasar Tunusia Ka’is Sa’id ya rusa majalisar dokokin kasa ne a ranar 30 ga watan maris kana ya kirayi gudanar da zaben yan majalisa a cikin watanni 3,

Kuma ya fitar da sanarwar ce a sa’ilin ganawarsa da cibiyar tsaron kasar yan sao’I bayan da majalisar ta gudanar da zamanta da ta saba inda ta amince da kudurin dake nuna adawa da mataken da ba’a saba ganin irinsa ba da ya dauka .

342/