Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

1 Mayu 2022

19:57:28
1253887

Rasha Ta Wargaza Wasu Makamman Da Amurka Da Turai Suka Baiwa Ukraine

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta cewa ta kai hari da makami mai linzami kan filin jirgin saman soji da ke kusa da birnin Odesa mai tashar jiragen ruwa, inda ta lalata titin jirgin da kuma wani rumbu da ke dauke da makamai da alburusai da Amurka da Turai suka kai wa Ukraine.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Rasha ta jima da takle gargadin kasashen yamma akan baiwa Ukraine makamai, wanda ta ce yana da matukar hadarin da zai iya hadassa yakin duniya na uku.

A nasa bangare Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya yi gargadin cewa Rasha na sake girke karin dakaru domin kai sabbin hare-hare gabashin kasar, inda ya ce gwamnatin Rasha ta kara tura wasu dakaru yankin Kharkiv da ke arewa maso gabashi a kokarin sake matsa kaimi a Donbass.

Rikicin Rasha da Ukraine dai ya shiga kwanansa na 67 a karshen wannan mako, kuma duk wata tattaunawa da ake da nufin warware rikicin ta kasa har kawo yanzu.

342/