Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

1 Mayu 2022

19:55:44
1253886

Guterres Ya Fara Ziyarar Aiki A Yammacin Afrika

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya isa Senegal, a wani ran gadi da ya soma a wasu kasashen yammacin Afrika.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - gana da shugaban kasar ta Senegla, Macky Sall, kana kuma shugaban kungiyar tarayyar AFrika a wannan karo.

Baya ga Senegal, Guterres, zai ziyarci kasashen Nijar da Najeriya.

Tasirin Rikicin Rasha da Ukraine, wanda ya haddasa hauhawan farashin man fetur da na alkama da kuma takin zamani, da mastalar tsaro, da tasirin canji yanayi da batun cutar korona na daga cikin batutuwan da Mista Guteress zai tattauna akansu.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar zai kuma yi tattaki zuwa Nijar inda zai kasance har zuwa ranar 3 ga watan na Mayu, kafin ya kammala rangadinsa a Najeriya a ranakun 3 da 4 ga dai watan.

Bayan tattaunawa da shugabannin kasashen uku da zai ziyarta, Guteress zai kuma gana da wakilan kungiyoyin fararen hula da shugabannin addinai.

342/