Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

1 Mayu 2022

19:21:15
1253854

Jami’an tsaro A Sudan Sun Tarwatsa Masu Zanga-zanar Cika Shekaru 3 Da Kisan Gilla Da Aka yi A Kasar

Rahotanni daga kasar Sudan sun bayyana cewa Jami’an tsaro sun harba hayaki mai sa hawaye kan masu zanga zangar da suka taru a babban birnin kasar, Khartum da ma sauran biranen kasar domin nuna adawarsu da mulkin soji a akasar, da kuma cika shekaru 3 da kisan killan da jami’an tsaro suka yi wa masu zanga –zanga.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Masu zanga zangar sun rufe manyan hanyoyin dake isa zuwa babban birnin tare da yin shinfida Abincin bude baki a kan titunan sai dai daf da shan ruwa jami’an tsaro suka tarwatsasu tare da fatattakarsu zuwa kan tituna

Akalla mutane 130 ne aka kashe tare da jikkata darurwa a kokarin murkushe masu zanga zangar adawa da juyin mulki da sojoji suka yi kamar yadda kungiyoyin kula da lafiya suka bayyana sai dai majiyar gwamnati ta nuna adadin wadanda aka kashe din basu wuce 87 ba,

Ana sa bangaren wakilin musamman na majalisar dinkin duniya a kasar Sudan Volker Perthes ya gargadi kwamitin tsaro na MDD a ranar 29 ga wtan maris cewa rashin cimma yarjejeniyar siyasa na kafa gwamnatin rikon kwarya ya haifar da tabarbarewa tattalin arziki da tsaro a kasar.

342/