Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

1 Mayu 2022

19:21:08
1253852

Ma’aikata A Najeriya Sun Gudanar Da Bukin Ranar Ma’aikata Ta Duniya

Shugaban majalisar Dattawa ta Najeriya Ahmad Lawal ya aike da sakon taya murna ga ilahirin ma’aika a fadin kasar, inda yayi musu fatan ganin an gudanar da shagulgulan wannnan rana lami lafiya,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Acikin wata sanarwa da ya fitar ta bakin mai taimakinsa kan harkokin yada larabai Ola Awoniyi ya jinjinawa Ma’aikatan kasar game da gudunmawar da suke bayarwa wajen gina kasa , kuma yayi kira da a gaggauta kawo karshen Takaddamar da ake yi tsakanin Gwamnati da Kungiyar malam Jami’oi ta Asuu a Najeriya don ganin an janye yajin aiki tare da bude makarantu dake rufe a yanzu haka.

Yace Ko shakka babu ma’ikatan Najeriya sun cancanci Yabo da jinjinawa game da namijin kokarin da suki ye wajen ci gaban kasar. Da kuma hadin kai da suka bawa gwamnati da sauran hukumomi wajen tunkarar kalubalen rayuwar zamantake da ke fama da su.

Dag karshe ya nuna cewa majaliasar za ta ci gaban da hada kai da kungiyar kwadago ta kasa wajen shawo kan matsalomin dake addabar Ma’aikata da ma Alummar kasar baki daya.

342/