Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

1 Mayu 2022

19:21:06
1253850

Musulmin Nijar Na Bikin Karamar Sallah Yau Lahadi

Al'ummar Musulmi a Jamhuriyar Nijar na bukukuwan Eid al-Fitr ko kuma karamar Sallah, a yau Lahadi, bayan kamalla azumin watan Ramadana.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Hakan ya biyo bayan tabbacin hango jinjirin watan Shawwal da Majalisar koli ta addinin musulunci ta Nijar ta bayar a daren ranar Asabar.

Kasashen Mali da Afghanistan ma sun gudanar da bikin karamar sallar a yau Lahadi.

Kasashen musulmi da dama irinsu Saudiyya da Najeriya, sun ce ba a ga watan Shawwal ba a ranar Asabar, abin da ke nufin zasuyi Azumin Ramadana 30 a bana.

342/