Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

30 Afirilu 2022

19:20:58
1253508

​Shugaban Ukrain Ya Bukaci Jawabi Ga Kasashen Kungiyar Tarayyar Afirka

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelesky, a karo na biyu, ya bukaci yin jawabi ga kasashen kungiyar tarayyar Afirka AU.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shafin yanar gizo na Labarai “Africanews” ya nakalto babban sakataren kungiyar ta AU Mr Musa Faqih yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa ya zanta da ministan harkokin wajen kasar Ukrain dangane da wannan batun ta wayar tarho.

Kafin haka dai kungiyar ta AU ta bayyana cewa tana bukatar a warware matsalar yaki a kasar ta Ukrain ta hanyar tattaunawa da kuma fahintar juna.

Banda haka a cikin makonnin da suka gabata shugaban kasar Senegak Makky Salla, ya kira shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho inda suka tattauna batun yakin na Ukrain, amma bai kira shugaba Zelesky ba. Wannan ne ya sa Zelesky ya fahinci cewa mafi yawan kasashen Afirka suna goyon bayan kasar Rasha a yakin na Ukrain.

Har yanzun dai babu tabbas ko kungiyar ta AU zata bawa Zelesky damar magana da su, wanda mai yuwa ya sami goyon bayan kasashen da basu dauki bangare har ya zuwa yanzu a yakin ba

Sai dai masana suna ganin ko da shugaban Zeleski ya yi magana da kungiyar da wuya ya shawo kan wasu kasashen Afirka , don irin dangantaka mai karfi dake tsakaninsu da Rasha a baya-bayan nan.

342/