Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

30 Afirilu 2022

19:20:55
1253507

​Mai Yuwa Tarayyar Turai Ta Hana Kasashen Kungiyar Sayan Makamashi Daga Kasar Rasha A Nan Gaba

Jaridar NewsYork time ta kasar Amurka ta bayyana cewa mai yuwa kungiyar tarayyar Turai ta haramtawa kasashen kungiyar seyan makamashi daga kasar Rasha saboda karya tattalin arzikinta don hanata ci gaba da yaki a kasar Ukrain.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar ta kara da cewa mai yuwa nan da ‘yan kwanaki wakilan kungiyar AU zasu kafa dokar wacce zata hana kasashen kungiyar sayan makashi daga kasar Rasha. Sai dai a fili yake kansu a rabe yake kan wannan batun don irin yadda suka dogara da kasar ta Rasha don samun makamashi.

Kasar Rasha ce kasa mafi arzikin isakar gas a duniya, inda a shekara ta 2020 ta sayarwa kasashen turai kashi 26% na makamashin da suke bukata.

Bayan an fara yaki a Ukrain ne kasashen na turai suka fara kauracewa makamashin iskar gas na kasar Rasha sannan suka fara nemansu a wasu kasashe masu arzikin man fetur da gas wadanda suka hada da kasashen yankin Tekun farisa, Najeriya, Kazakisatn da Azebajan.

342/