Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

30 Afirilu 2022

13:40:36
1253425

Muzaharar Kudus A Zariya Ta Firgita Isra'iliyawa;

Jami'an Tsaron Nijeriya Sun Raunata Mutum Takwas

Kamar yadda aka saba a duk shekara, fiye da shekaru Arba'in ana gudanar da muzaharar Kudus ta duniya a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky a duk ranar Juma'ar ƙarshen kowacce Ramadan, a bana ma 'yan'uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na garin Zariya da kewaye ba su yi ƙasa a guiwa ba inda aka gudanar da wannan muzaharar.

Sakamakon tuɗaɗar 'yan'uwa Musulmi a garin na Zariya, an raba muzaharar ta bana zuwa gida biyu; a inda wadansu suka taso daga Agoro dake Tudun Wada Zariya, wasu kuma suka taso daga Masallacin Kwata dake Sabon Garin Zariya.

Muzaharar ta soma gudana ne jim kadan da kammala sallar Juma'a bayan 'yan'uwa sun halarci sallar ta Juma'a. Inda aka soma Kabbarori da salatin Annabi Sallallahu Alaihi Wa'alihi Wassalam, sannan aka hau sahu cikin nizami da lumana daga Masallacin Kwata dake Sabon Garin Zariya.

342/